Monday 11 January 2010

MU KYAKYATA SECTION :TWO STORIES

A asibitin mahaukata ne, sai wani mahaukaci, mai suna dan-kawu ya tsunduma cikin wani katon tankin ruwa. Da wani mahaukacin, wai shi Sallau ya hangoshi yana neman mutuwa, sai nan take yaje ya tsamo shi. Jin wannan labari sai babban likitan asibitin ya zata lallai Sallau ya warke, kuma ya kamata a yi masa dubawar karshe a sallameshi. likita ya kirashi yace, 'Amma fa Sallau ka birgeni yadda ka tsamo Dan-kawu daga tankin ruwa ka ceci ransa. saboda hak..... kafin likita ya karasa magana, sai ga wani a guje yana cewa: 'ai dan-kawu ya rataye kansa ya mutu'. Jin haka sai Sallau yace,' Kash! Wallahi ba kashe kansa yayi ba. NINE NA RATAYESHI DON YA BUSHE'.....lol inkai ne likitan yaya za kayi? ********************************************MR BRUKER DA YARSA******** Mr Bruker ne ya hango yar sa tana gogewa karensu baki da Brush dinsa. Yace, ke! me kikeyi haka ne! Tace ina gogewa HERO bakin sa ne. Kada ka damu DADDY, in na gama zan mayar maka da BURUSHINKA kamar KULLUM! in kaine yaya za kayi?

2 comments: