Monday 11 January 2010

Barayi Da Liman: By: Misbah M. B

Anyi wasu barayi guda biyu da suke satar lemo,kullum in suka sato sai suje makabarta su ajiye sai bayan dare yayi sai su je su raba kayansu. rananna suna cike suna rabawa. to dama in ana rabon daya ba yan daya ake yi don kar a cuci wani.to wani dan kwalu (me shan tabar wiwi) ya zo jikin makabarta domin ya dan je sky sai yaji barayin nan suna rabo kai daya ni daya..... haba hankalinsa ya tashi tuni ya koma cikin gari ya fadawa liman wallahi ga malaiku can a cikin makabarta suna diban yan wuta da yan aljanna... haba malam ni tun da nake ban tabajin malaiku sun je makabarta ba amma muje na gani. da zuwansu sai sukaje ana ta rabo ni daya kai daya.to dama lokacin da suke shigo da kayan wasu sun zube a bakin get na shigowa.sai daya daga cikin barayin yace to ga guda biyu can a waje sai ka dau daya nima na dau daya......... haba da jin haka sai liman ya cika wandon sa da iska..............................

1 comment: