Thursday 7 January 2010

Lawal Auwal Sani Danbuzu SPIRIT: MAGANI KO ALJANI

SPIRIT: MAGANI KO ALJANI: A kwana-kwanan nan ba da dadewaba anagobe zan dawo Musawa daga Calabar, wata baiwar Allah mai suna Ekaite dake zaune anan unguwar Bogobiri tayi wani abu shi ba abin haushiba ba kuma na dariyaba.in dai takaice maku labari, a wata asabarne bayan an gama wani bikin binne gawa a unguwar, dare yayi kowa ya kwanta, kawai sai ta tsiri aske duk wani gashi dake wani lungu a jikinta. watakila saboda shagalin bikinta da za'a tashi da shi washe gari Lahadi. bayan ta gama da abinda ya shafi hammata da sauransu, ta shagala da aske gashin mara, kuma ga barci yana neman danneta asabili da gajiyar zurga-zurgar da ta wuni yi, ba tare da tayi auneba kawai sai taji wani abu zuuu! har tsakiyar kanta gami da radadi daga kasanta, dubawar da zatayi haka, sai taga jini yanata kwarara daga kasan mararta, ashe yankewa tayi a gefen clitoris dinta a garin kwakulo gashi ta aske. "O! my God i don destroy am" kalmar da ta furta kenan cikin rudewa. kawai sai ta tashi tayi daka a guje tare da fadin "Thank you God". hakan ta faru ne bayan ta tuna wajen da babanta ke ajiye kwalaben spirit, da yake ma'aikacin jinyane. kash! rashin tabbas na NEPA sai kawai suka dauke wuta bayan ta gama antaya spirit din harma yayi ambaliya cikin wajen da yafi ko ina tsada ajikinta ba tare da ta saniba saboda rudewa. asabilida shigar spirit gurinda bai kamata ya shigaba sai radadi da zugin yama ci uban nada, ga kuma duhunda NEPA ta haddasa. Sai ta ruga dakin girki cikin dimauta domin dakko ashana. Dakkowarta keda wuya sai ta kyasta domin ta haska wajen domin taga abinda ke faruwa. Kasan spirit kamar fetur yake kanga ashanar keda wuya ji kake butt!! gobara ta tashi a wajen. Ekaite kuma a iya saninta ta san spirit dinnan da ta saka shine ya haddasa gobarar, saboda haka bata san lokacinda ta fara ihu tana fadin "spirit! spirit!! spirit!!!" ba, su kuwa mutane da suka ji ana fadin spirit cikin ihu da kuka, kuma gashi 'yan sa'o'i kalilan bayane akayi bikin binne gawa tareda 'yan tsafe-tsafe sai suka zaci spirit da take kira na Aljan ne ba na maganiba. Saboda haka ba wanda ya ko leko don tsoro. Nan dai wannan waje ya kone kurmus, aurenda bai yiwu washe gari kenanba. Na dai dawo Musawa na barota a gadon Asibitin Koyarwa na Jami'ar Calabar. Don ko da naje dubiya ban iya yi masa kallo na biyuba, domin ya riga ya gama cakalkalewa ya kwabe tamkar gwalagwajen tumatir. Daga baya ne ma ina gida nake samun labarin wai mijin ya fasa wai bai son konannen abu wai ya nakasa, launinsa da.. sun sauya. To! Allah ya kyauta. Amin suma amin

No comments:

Post a Comment