Sunday, 17 January 2010

KAFIN KAGA BIRI; BIRI YA GANKA

Wasu daliban Jami'ane suka tafi Night
club sukai abin nan da ake kira da
TILL-DAWN. Kuma sun san suna da
jarrabawa washe gari, gashi kuma
basuyi karatu ba. Saboda haka suka
shirya yiwa farfesa karya. Sai suka
sanya kaya masu datti kuma suka bata
jikinsu da bakin mai. Da suka je ofis
din Farsesa sai suka ce masa jiya da
daddare sunje bikin abokinsu a wani
kauye mai nisan 100km, a kan
hanyarsu ta dawowa sukai faci, shine
suka turo motar sai yanzu suka
dawom; saboda haka suna neman
Farfesa yai musu afuwa su dan dawo
hayyacinsu kafin su zana exam din.
Farfesa da yaji haka sai ya tausaya
masu yace suje nan da kwana uku su
dawo.
Bayan kwana 3 suka dawo, farfesa yace dasu tun da dai wannan jarabawa ce ta musammman kowanne daya d aga cikin su hudun nan za a sashi a aji daban-daban baza a hada suba. Dayake sun yi karatu sosai kuma sun shirya basu damuba sukace sun yarda.....
Jarabawar dai tana da Jimillar maki 100 kuma ta kunshi tambayoyi Guda biyar. Amman da sharadin idan daya daga cikinsu ya amsa ba daidai ba to dukkan su hudun zasu samu zero mark.

Tambay ta daya:
Rubuta sunan ka da
lambarka...(20point)
Tambaya ta 2:
Ya sunan Ango da Amaryar da kuka je
bikin su (30marks)
Tambaya ta 3:
Wacce irin Mota kuke tukawa
(20marks)
Tambaya ta 4: Waye
acikinku direban Motar (15point)
Tambaya ta 5: Tayar wanne bangare
ce tai facin? (15marks)
In ka/ki na cikin su ya za ka/ki yi?...lol

Monday, 11 January 2010

MU KYAKYATA SECTION :TWO STORIES

A asibitin mahaukata ne, sai wani mahaukaci, mai suna dan-kawu ya tsunduma cikin wani katon tankin ruwa. Da wani mahaukacin, wai shi Sallau ya hangoshi yana neman mutuwa, sai nan take yaje ya tsamo shi. Jin wannan labari sai babban likitan asibitin ya zata lallai Sallau ya warke, kuma ya kamata a yi masa dubawar karshe a sallameshi. likita ya kirashi yace, 'Amma fa Sallau ka birgeni yadda ka tsamo Dan-kawu daga tankin ruwa ka ceci ransa. saboda hak..... kafin likita ya karasa magana, sai ga wani a guje yana cewa: 'ai dan-kawu ya rataye kansa ya mutu'. Jin haka sai Sallau yace,' Kash! Wallahi ba kashe kansa yayi ba. NINE NA RATAYESHI DON YA BUSHE'.....lol inkai ne likitan yaya za kayi? ********************************************MR BRUKER DA YARSA******** Mr Bruker ne ya hango yar sa tana gogewa karensu baki da Brush dinsa. Yace, ke! me kikeyi haka ne! Tace ina gogewa HERO bakin sa ne. Kada ka damu DADDY, in na gama zan mayar maka da BURUSHINKA kamar KULLUM! in kaine yaya za kayi?

Barayi Da Liman: By: Misbah M. B

Anyi wasu barayi guda biyu da suke satar lemo,kullum in suka sato sai suje makabarta su ajiye sai bayan dare yayi sai su je su raba kayansu. rananna suna cike suna rabawa. to dama in ana rabon daya ba yan daya ake yi don kar a cuci wani.to wani dan kwalu (me shan tabar wiwi) ya zo jikin makabarta domin ya dan je sky sai yaji barayin nan suna rabo kai daya ni daya..... haba hankalinsa ya tashi tuni ya koma cikin gari ya fadawa liman wallahi ga malaiku can a cikin makabarta suna diban yan wuta da yan aljanna... haba malam ni tun da nake ban tabajin malaiku sun je makabarta ba amma muje na gani. da zuwansu sai sukaje ana ta rabo ni daya kai daya.to dama lokacin da suke shigo da kayan wasu sun zube a bakin get na shigowa.sai daya daga cikin barayin yace to ga guda biyu can a waje sai ka dau daya nima na dau daya......... haba da jin haka sai liman ya cika wandon sa da iska..............................

Thursday, 7 January 2010

Auwal Ibrahim LABARIN SARKIN ROWA DA BAMAGUJE

A wani dan kauye mai suna Lunkum.Anyi wani mutum marowaci mai suna Tsurkuli, wanda saboda tsabar rowarsa har ake masa lakabi da sarkin rowa don ko Daddawa ya siya sai ya kukullata a leda ya ba matarsa har sai ta kai sati. wata rana ya je kasuwa ya siyo naman kai, a kayi masa dabge.Ranar aka ci sa'a ya fito da shi zaure,ya bude kenan zai fa ra ci sai wani abokinsa Bamaguje ya kutso kansa cikin gidan,ko da ya ganshi sai ya ji kamar ya koma dashi gida,amma dai ya da ke sai ya ce masa a fusace.kai wane irin mutum ne ya za ka shigo ma na gida ba sallama.sai Bamaguje ya ce kamanta ni ba musulmi bane.sai sarkin rowa yayi masa gatse yace:in za ka ci?kazo mu ci.sai Bamaguje ya sa hannu ya fara ci ya na hannu ba ka hannu kwarya.ya ra sa hanyar da zai masa wayo.Can sai wata dabara ta fa do masa.sai yace da shi Laa kalli sama taurari suna gudu,sai bamaguje ya kalli sama amma hannunsa ya na cikin kwanon da ya ga ya gane.sai yai zumbur ya mike a fusace ya shiga gida ya na ta yan zage-zage.Da matarsa ta ga abin na shi ya yi yawa sai ta tambaye me ya faru sai ya kwa she ya gaya mata abinda ya gudana tsakaninsa da Bamaguje.Sai matar tace:Uhm maganinka ke nan daman an ce DUK WANDA BAI BAUTAWA ALLAH BA ZAI BAUTAWA ALLARO..

Labarin Alti Da KUtare BY: Mustapha A Sagir

Azamanin mai tsaho daya shude anyi wani tsoho mai suna Alti. Alti mutum ne mai girman kai, zafinrai da kuma rigima. Wata rana anyi ruwa an dauke sai ALti yaje kasuwa don yasai takarkari, shigarsa keda wuya sai jakin wani kuturu yai tutsu ya kada wannan kuturu ana atare atare sai Alti ya tunada tsohon tsiminsa, basai ya tari jaki gaba-da-gaba ba. Kai kuma aura (jaki) kana zuwa sai ka kama cunar rigar Alti kai taja kana cizo har tai kaca-kaca. Kuturu na zuwa sai yasa gundulmi garin dukan jaki sai ji kake fas a kan Alti. Alti yai sama ya fado asume, yan sannu-sannu suka lalubeshi tas. Koda Alti ya farfado yaga ba kuturu ba jaki, kuma ba kudi sai ya dinga zagayawa kasuwa in yaga kuturu sai ya tambaya kaine mai jaki, sai ya wuce, hala sai ga wata tsohuwar kuturuwa tai yawo bata samu ko aniniba, koda ya tambayeta sai tace eyeh nice mai jaki. Gogan naku kawai sai ya rufe kuturwa da duka. Koda sauran kyadayen sukaga haka, kawai sai suka rufeshi da duka da mangari... Da kyar aka kwa ceshi. Koda aka nutsa, sai Alti yace shi dai ya hakura amman lallai kuturunnan na farko sai ya nuna mishi gudumar daya dakeshi da ita..hahahhahah kurunkus

Bahaushe da Inyamuri BY: Mustapha A Sagir

A zamanin da ya shude lokacin mulkin mallaka daf da samun yan cin kai.... Inyamuri da Bahaushe suka shiga mota domin zuwa unguwa a jahar kano. Inyamuri sai ya sanarda kwandasta cewar lallai in aka zo Lamido crescent ya sanar dashi don ananne zai sauka. Kai kuma Malam Bahaushe sai ka kife inyamuri da mari kace: don ubanka Lamido ba KIRISTA bane. Sai rigima ta barke, abu kamar wasa sai gaban kuliya manta sabo. Koda Alkali yaji tabakin kowa, sai yace: To Inyamuri kace akaika LAMIDO MUSULIM sai karama marinka. Amman Inyamuri yace; Chineke I n o go say LAMIDO muslim the BUS may take me to different location...hahahhaha

Lawal Auwal Sani Danbuzu SPIRIT: MAGANI KO ALJANI

SPIRIT: MAGANI KO ALJANI: A kwana-kwanan nan ba da dadewaba anagobe zan dawo Musawa daga Calabar, wata baiwar Allah mai suna Ekaite dake zaune anan unguwar Bogobiri tayi wani abu shi ba abin haushiba ba kuma na dariyaba.in dai takaice maku labari, a wata asabarne bayan an gama wani bikin binne gawa a unguwar, dare yayi kowa ya kwanta, kawai sai ta tsiri aske duk wani gashi dake wani lungu a jikinta. watakila saboda shagalin bikinta da za'a tashi da shi washe gari Lahadi. bayan ta gama da abinda ya shafi hammata da sauransu, ta shagala da aske gashin mara, kuma ga barci yana neman danneta asabili da gajiyar zurga-zurgar da ta wuni yi, ba tare da tayi auneba kawai sai taji wani abu zuuu! har tsakiyar kanta gami da radadi daga kasanta, dubawar da zatayi haka, sai taga jini yanata kwarara daga kasan mararta, ashe yankewa tayi a gefen clitoris dinta a garin kwakulo gashi ta aske. "O! my God i don destroy am" kalmar da ta furta kenan cikin rudewa. kawai sai ta tashi tayi daka a guje tare da fadin "Thank you God". hakan ta faru ne bayan ta tuna wajen da babanta ke ajiye kwalaben spirit, da yake ma'aikacin jinyane. kash! rashin tabbas na NEPA sai kawai suka dauke wuta bayan ta gama antaya spirit din harma yayi ambaliya cikin wajen da yafi ko ina tsada ajikinta ba tare da ta saniba saboda rudewa. asabilida shigar spirit gurinda bai kamata ya shigaba sai radadi da zugin yama ci uban nada, ga kuma duhunda NEPA ta haddasa. Sai ta ruga dakin girki cikin dimauta domin dakko ashana. Dakkowarta keda wuya sai ta kyasta domin ta haska wajen domin taga abinda ke faruwa. Kasan spirit kamar fetur yake kanga ashanar keda wuya ji kake butt!! gobara ta tashi a wajen. Ekaite kuma a iya saninta ta san spirit dinnan da ta saka shine ya haddasa gobarar, saboda haka bata san lokacinda ta fara ihu tana fadin "spirit! spirit!! spirit!!!" ba, su kuwa mutane da suka ji ana fadin spirit cikin ihu da kuka, kuma gashi 'yan sa'o'i kalilan bayane akayi bikin binne gawa tareda 'yan tsafe-tsafe sai suka zaci spirit da take kira na Aljan ne ba na maganiba. Saboda haka ba wanda ya ko leko don tsoro. Nan dai wannan waje ya kone kurmus, aurenda bai yiwu washe gari kenanba. Na dai dawo Musawa na barota a gadon Asibitin Koyarwa na Jami'ar Calabar. Don ko da naje dubiya ban iya yi masa kallo na biyuba, domin ya riga ya gama cakalkalewa ya kwabe tamkar gwalagwajen tumatir. Daga baya ne ma ina gida nake samun labarin wai mijin ya fasa wai bai son konannen abu wai ya nakasa, launinsa da.. sun sauya. To! Allah ya kyauta. Amin suma amin