Thursday 7 January 2010

Auwal Ibrahim LABARIN SARKIN ROWA DA BAMAGUJE

A wani dan kauye mai suna Lunkum.Anyi wani mutum marowaci mai suna Tsurkuli, wanda saboda tsabar rowarsa har ake masa lakabi da sarkin rowa don ko Daddawa ya siya sai ya kukullata a leda ya ba matarsa har sai ta kai sati. wata rana ya je kasuwa ya siyo naman kai, a kayi masa dabge.Ranar aka ci sa'a ya fito da shi zaure,ya bude kenan zai fa ra ci sai wani abokinsa Bamaguje ya kutso kansa cikin gidan,ko da ya ganshi sai ya ji kamar ya koma dashi gida,amma dai ya da ke sai ya ce masa a fusace.kai wane irin mutum ne ya za ka shigo ma na gida ba sallama.sai Bamaguje ya ce kamanta ni ba musulmi bane.sai sarkin rowa yayi masa gatse yace:in za ka ci?kazo mu ci.sai Bamaguje ya sa hannu ya fara ci ya na hannu ba ka hannu kwarya.ya ra sa hanyar da zai masa wayo.Can sai wata dabara ta fa do masa.sai yace da shi Laa kalli sama taurari suna gudu,sai bamaguje ya kalli sama amma hannunsa ya na cikin kwanon da ya ga ya gane.sai yai zumbur ya mike a fusace ya shiga gida ya na ta yan zage-zage.Da matarsa ta ga abin na shi ya yi yawa sai ta tambaye me ya faru sai ya kwa she ya gaya mata abinda ya gudana tsakaninsa da Bamaguje.Sai matar tace:Uhm maganinka ke nan daman an ce DUK WANDA BAI BAUTAWA ALLAH BA ZAI BAUTAWA ALLARO..

No comments:

Post a Comment