Sunday 17 January 2010

KAFIN KAGA BIRI; BIRI YA GANKA

Wasu daliban Jami'ane suka tafi Night
club sukai abin nan da ake kira da
TILL-DAWN. Kuma sun san suna da
jarrabawa washe gari, gashi kuma
basuyi karatu ba. Saboda haka suka
shirya yiwa farfesa karya. Sai suka
sanya kaya masu datti kuma suka bata
jikinsu da bakin mai. Da suka je ofis
din Farsesa sai suka ce masa jiya da
daddare sunje bikin abokinsu a wani
kauye mai nisan 100km, a kan
hanyarsu ta dawowa sukai faci, shine
suka turo motar sai yanzu suka
dawom; saboda haka suna neman
Farfesa yai musu afuwa su dan dawo
hayyacinsu kafin su zana exam din.
Farfesa da yaji haka sai ya tausaya
masu yace suje nan da kwana uku su
dawo.
Bayan kwana 3 suka dawo, farfesa yace dasu tun da dai wannan jarabawa ce ta musammman kowanne daya d aga cikin su hudun nan za a sashi a aji daban-daban baza a hada suba. Dayake sun yi karatu sosai kuma sun shirya basu damuba sukace sun yarda.....
Jarabawar dai tana da Jimillar maki 100 kuma ta kunshi tambayoyi Guda biyar. Amman da sharadin idan daya daga cikinsu ya amsa ba daidai ba to dukkan su hudun zasu samu zero mark.

Tambay ta daya:
Rubuta sunan ka da
lambarka...(20point)
Tambaya ta 2:
Ya sunan Ango da Amaryar da kuka je
bikin su (30marks)
Tambaya ta 3:
Wacce irin Mota kuke tukawa
(20marks)
Tambaya ta 4: Waye
acikinku direban Motar (15point)
Tambaya ta 5: Tayar wanne bangare
ce tai facin? (15marks)
In ka/ki na cikin su ya za ka/ki yi?...lol

1 comment: